Ɗaukaka (#11717)

Yā Allah, ka sanyaya, kuma ka farinta rūhuna. Tsarkaka zūciyāta. Haskaka hankalīna. Nā damƙa dukan al’amurāna cikin hannunka. Kai nē shūgabāna da maɓūyata. Bā nā son zama cikin baƙin rai da hushi. Nā fi son zama cikin farin ciki da murna. 
Yā Ubangijina, bā ni son zato da azāba su māmāye ni.
Yā Allah, ka fi sō nā, da yadda nike son kaina. Nā dawwama garēka, yā Ubangijina.
Baha’u’llah

Yā Allah! Yā Allāna! Gā bāwanka nā nufa wajenka, kuma da zūciya guda, yana rātsa hamādar ƙaunarka, kan hanyar bauta maka, cikin jiran taimakonka, bisa ga tsammānin yalwarka, amince da īkonka, kuma tāre da ni’imarka.
Yā Allāna! Ka sā ƙaunar bāwan nan nāka a garēka, ta ƙāra fīfīta, kullum, kada ya daina yabā ka, kuma hamzarinshi wajen ƙaunarka, ya ƙāra cī gaba. Hakīka! Kai nē mai saukar da ni’ima, yalwarka bā ta da iyāka.
Bā wani Allah sai kai, mai jinƙai, mai rahama.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Ɗaukaka (#11718)

Ka ƙirƙiro mani zūciya mai tsarki yā Allāna, kuma ka tabbatar mani da kyaukyāwan lamiri. Yā abun bēgēna, a cikin ƙudurarka, ka ƙarfafā ni bisa hanyarka, yā abun ƙaunata. Ka sā hasken ɗaukakarka ya būɗe mani hanyā zuwa garēka. 
Yā kai mafārin duk bukātūna. A cikin girmanka mabuwāyi, ka ɗaukaka ni a samāniyar tsarkakēwarka, yā kai mafārin fāruwāta, ina rōƙon ka, a cikin zamancēwarka marar iyāka, ka sā in rāyu cikin farin ciki, yā kai da kake Allāna. Ka saukō mani kwanciyar hankali, yā kai abōkin zamāna, ka sā annurin fuskarka ya kai ni nēsa da duk wani abu in bā kai ba, yā Ubangijina, ka sā lābārin tabbatarka da ɗayantakarka, su cika zūciyāta da murna. Yā kai mai girma, ayyananne, wanda ya tabbata gaba da kōmi, kai nē mai cikakken sirran cikin ban māmāki.

Yā Ubangijina ! Ka sā kyaukyāwar alāmarka ta zamanto abuncīna, kusancinka abun shāna, ƙaunarka gūrina, yabonka abun aikatāwāta, tunāninka abōkin tafiyāta, ƙudurarka kāriyāta, wurinka mabartāta, kuma ka sā gidāna ya zama wurin da ka shāre duk wasu abūbūwan da suka tsayar waɗanda yāna ta kāre su da kai.
A gaskiya kai nē mabuwāyi, jalla babban sarki, ƙadīran.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Ɗaukaka (#11719)

Dukan yabo ya tabbata a garēka yā Ubangiji Allāna ! Ina rōƙon ka, da sūnanka mai martaba da aka tsare cikin kurkukun birnin Akka, wanda ya fāɗā hannun maƙiyansa, kuma la’anannu suka zāre masa takubbansu, ka bā ni ƙarfin da zan zama tsayayye cikin addininsa, kuma in jūya kallōna wajensa, ta yanda bā wanda ya isa ya karkatar da ni.
Nā shaida yā Ubangijina cēwa, yā bāyar da ransa bisa hanyarka, kuma don tsananin ƙaunarka, yā gwammace da wahala. Bābu cin mutuncin da ba a masa ba, don yā bayyanar da mulkinka zuwa ga bāyunka, kuma yā ɗaukaka kalmarka gaban halittarka. Kō da yake, matsalōli suna ƙāra cī gaba, kuma darūrar da ka zubo masa tā māmāye shi ta kō’ina, sai ya ƙarfafa cikin tunāninka, har ya zamanto duk yawan waɗanda suka wātsar da alāmunka, kuma su ka ƙi bāda gaskiya a garēka, sun daina bā shi tsōro.
Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, a bisa darajarsa da duk abunda yake nāsa nē, ka sā ƙaunāta ta tabbata a garēshi, kamar yanda ƙaunarsa ta tabbata a garēka. 
Nā shaida da cēwa, ƙaunarsa ƙaunarka cē, bayyanarsa bayyanarka ce, haskensa haskenka nē, kuma addininsa addininka ne.
Kada ka hana mani yā Ubangijina, abun da ka mallaka, kada ka dāmu don nā mance abun da kake sō a rānēkunka. Hakīka, kai nē mabuwāyi, maɗaukakin sarki, jalla mafi basīra.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

