Ziyāra (#11757)

*Wannan āyā, ana jan ta a ƙabarin Baha’u’llah, kō na Bab (tsīra da aminci su tabbata a garēsu). Wanda yake sō, yana iya karantā ta, rānēkun haifuwarsu.
Yabo dake dangance da zamantakēwarka mai martaba, kuma da mahibbar da ta haskō daga ƙyalƙyalin kyāwonka, su tabbata a garēka, yā kai da kai nē alāmar girma, da kai nē sarkin dawwama har abada, kuma da kai nē Ubangijin duk abūbūwan dake ƙasa da sammai !
Nā shaida cēwa, ta garēka nē, mulkin Ubangiji Allah, martabarsa da girmansa, suka bayyana, taurārun sāfiyar kyaukyāwar dauri, suka baza haskensu da bā ya shūɗēwa, cikin samāniyar kudurinka, kuma kyāwon wanda bā ya ganuwa, ya haske jiririn halitta. 
Nā shaida kuma da cēwa, daga rubūtun alƙalaminka guda, sai umarninka « kasance » ya aikata, ɓōyeyyen gaibun Ubangiji Allah ya bayyana, ka rāya duka halittu, kuma duka wahāyi ya sauko.
Nā shaida cēwa, ta kyāwonka nē, kyāwon wanda shīnē abun yabo ya bayyana, kuma ta fuskarka cē, fuskar wanda shīnē abun ƙauna ta fitō hīli, kuma da kalmā guda, ka ƙayyada matsayin duk halitta, ka ɗaukaka wanɗanda suka yi īmāni har zuwa ƙōli, kuma ka jēfa kāfirai cikin rāmi mai zurfi.
Nā shaida cēwa, wanda ya amince da kai, yā amince da Allah Ubangiji Subahānahu wa ta āla, kuma wanda ya kai garēka, yā kai ga Ubangiji Allah. Albarka ta tabbata ga wanda ya yarda da kai kuma da alāmunka, ya gwada tawāli gaban martabarka, kuma ya sāmu sāduwa da kai, ya cinma bukātunka, ya jāƙuɗo kusanka, kuma ya durƙusa gaban karagarka.
Hallaka ta tabatta : ga wanda ya ɗauki zunubi garēka, ya yi wātsi da kai, ya yi jīfa da alāmunka, ya ƙi yarda da martabarka, kuma ya tāshi ya kai maka hari, ya gwada girman kai a gabanka, ya ƙi karɓar shaidōdinka, ya kēɓēwa dōkōkinka, ya yi adāwa da ikonka, ya shiga cikin kāfiran nan da sūnāyansu suke rubūce bisa tsarkakkun allunan ƙudurarka.
Daga dāmar rahamarka da alhērinka, ka sauko mani, yā Allah Ubangijina, abun ƙaunāta, tsarkakakkar bazarar alhērinka, dōmin ta ƙēɓē ni da nī kaina, kuma da dūniya, sabōda ta jāgōrancē ni wajen dandalin kusantarka da kaiwa garēka. Kana da īkon aikata abun da ka ga dāma, hakīka, kai nē bisa ga kōmi da kōwa.
Ambatar Ubangiji Allah, da yabonsa, ɗaukakarsa da girmansa su tabatta a garēka, yā kai wanda kai nē kyāwonsa ! Nā shaida da cēwa, bābu idon halittar da ya kalli wanda aka zālunta kamar kai. Duk rāyuwarka, an zunduma ka cikin tēkun rūdāni. A wani lōkaci, an ɗaure ka da sarƙa da mari, a wani lōkaci kuma, maƙiyyanka sun zāre maka takubbansu. Amma, duk da haka, kā gayyaci mutāne, da su bi umarnin da wanda shīnē al’alīmu, mai hikima maras iyāka, ya sauko a garēka.
Ina rokon Ubangiji, da ya karɓi rūhūna, tamkar tōshi, dōmin wahalōlin da ka gabāta, kuma ya amshi raina sabōda adāwar da aka maka. Ina roƙon ka, don darajarka da waɗanda fuskarsu ta sāmu ƙyalƙyalin hasken fuskarka, waɗanda don matuƙar ƙaunarka, suka karɓi duk abūbūwan da ka umarcē su da yi, ka kēta lābilen da ya raba ka da halittarka, kuma ka bā ni alhērin dūniya da na lāhira. A gaskiya, kai nē al’azīzu, kai nē al’alīyu, mafi ɗaukaka, mai gāfartāwa har kullun, mai jin-ƙai.
Yā Ubangiji Allāna, ka albarkatar da itāciyar Ubangiji, da ganyenta, da rassunta, da tsironta, da karanta, da ƴāƴanta, har iyākar tsawon sūnāyenka māsu martaba, da laƙanunka mafi ɗaukaka. Ka kāre su, da harin maƙiya, da rundunōnin azzālumai. A gaskiya, kai nē al’azīzu, al ƙādiru. Yā Allāna, ka albarkatar da bāyinka maza da māta, da suka isō garēka. A gaskiya, kai nē mai rahama, wanda alfarmarsa bā ta da iyāka.
Bābu wani Allah illa kai, mai gāfartāwa a kullun, mayalwaci.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Ziyāra (#11758)

*Wannan āyā, ana jan ta a ƙabarin Abdul Baha, amma kuma mutun yana iya jan ta, don rāɗin kansa.
*Idan kā yi wannan addu’a cikin īmāni da tawāli, haka nā sā zūciyar Abdul Baha ta jī dāɗi, kamar dai kana gabansa nē.
Shīnē Al majīdu.
Yā Allah, Allāna ! Cikin tawāli da sujāda, nā ɗaga hannuwāna wajenka, cikin rōko, kuma nā ɗōra gōshīna bisa ƙūrar balbālinka, wanda ya fi ƙarfin duk wani sanin masani da yabon duk abun da yake ɗaukaka sūnanka. Ka kalli da idon rahama, wannan ƙasƙantaccen bāwan nāka kāsashē, da yake gaban ƙōfarka, kuma ka zunduma shi cikin tēkun alfarmarka maras ƙārēwa.
Yā Ubangiji ! Gā bāwanka matalauci ƙasƙantacce, yana rōƙo cikin sūjada, kāme cikin hannunka, yana addu’a cikin armashi da yarda a garēka, idānuwansa cike da hawāye gaban fuskarka. Wannan bāwa, yana kiranka, yana rōƙonka da cēwa : « Yā Ubangiji Allāna, ka ƙarfafā ni cikin bautāta a garēka, ka haske gōshīna da hasken ibāda a cikin dandalinka mai tsarki, kuma da hasken addu’a cikin daularka mai girma. Ka taimakē ni, in yi wātsi da kōmi gaban dakalin ƙōfarka ta samāniya, kuma in dangana da kōmi a cikin balbālinka mai tsarki.
Yā Ubangiji, ka sā ni in shā cikin luddan dangana, ka sā mani rīgarta, kuma ka zundumā ni cikin tēkunta. Ka maida ni ƙūra bisa hanyar masōyenka, ka yardē mani in bāda tōshin raina ga ƙasar da ka darajanta da sāwun zāɓāɓɓu dake bin hanyarka, yā kai Ubangijin ɗaukaka cikin ɗaukaka.»
Ta wannan addu’a, bāwanka nā kiranka cikin assuba da dare. Ka ƙarɓi buƙātar zūciyarsa, yā Ubangiji ! Ka haskē, kuma ka sā murna cikin ransa, ka wāye rūhunsa, dōmin ya kyautatāwa umarninka da bāyinka.
Kai nē mayalwaci, mai jin-kai, mai karāma, mai rahama, mai kulāwa.

-`Abdu'l-Bahá
-----------------------

