Yabo (#11722)

Dukan yabo yā tabbata a garēka, yā Allah Ubangijina ; kai da kake tūshen girma da ɗaukaka, sarauta da mulki, natsuwa da alhēri, mai ban tsōro da īko. Ga wanda ka ga dāma, ka kan jāwo shi, kusa da mahīhīcin tēkunka mai girma. A kan wanda ka nufa, ka kan sanarshē shi da sūnanka na fil azal. Ga duka waɗanda kē sama da ƙasa, bā wanda zai iya tsayāwa ga nufinka mai girma. Tun fil azal, kā yi mulkin halittarka, kuma zā ka ci gaba da mallaƙar abin da ka hālittō da īkonka. Bā wani Ubangiji sai kai, mafi girma, mafi ɗaukaka, mafi īko da basīra.
Ka haskaka huskōkin bāyinka, dōmin su gan ka, ka wanke zukātansu, dōmin su jūya zuwa sāmun ni’imarka, kuma su bāda gaskiya ga wanda ya bayyana asīranka da babbar alfurmarka.
Bā shakka, kai nē Ubangijin duka dūniya. Bā wani Allah sai kai, mai nasara, mai mallaƙar kōmi.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Yabo (#11723)

Yā Allāna, abun ƙaunāta, majibincīna, abun bukātāta! Da wane irin halshē zan iya bayyana iyākacin gōdiyāta zuwa  garēka ? Ina cikin duhu, kā wāyar da ni. Nā huta daga hanyarka, kā maidō ni cikin alfurmarka. Nā zamana kamar matacce, kā rāyar da ni da ruwanka mai rāyarwa. Nā ƙēƙashe, ka falfaɗō ni da ruwan samāniyar kalmarka da suka zubo daga alkalamin rāhimi.
Yā kai ƙaddara ! Bābu sāmun wata rāyuwa in bā ƙalƙashin alhērinka bā. Kar ka kauce mana da kyautatāwarka, kuma kar ka kai mu nēsa da kōgin rahamarka. Ina rōƙon ka taimakē ni, a kullum, kuma a kō’ina, ina rōƙon ka, daga samāniyar alfurmarka, ka sauko mani da wannan alfurma tāka ta tun fil azal.
A gaskiya, kai nē Ubangiji mayalwaci, mai mallaƙar kōmi da kōwa.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Yabo (#11724)

Ka cē : ɗaukaka ta tabbata a garēka, kai da ka sā duka waliyyai suka yarda da kāsāwarsu gaban cikakken īkonka, kuma ka sā kōwane manzonka, ya tabbata cēwa, shi bā kōmi nē ba gaban managartacciyar ɗaukakarka marar iyāka.
Ina rōƙon ka, don girman sūnanka, wanda ya būɗe ƙōfōfin samāniya, kuma ya cika rūhunan dake samāniya da ƙaunarka, ka sā ni in dāce don in bautā maka, kuma ka bā ni ƙarfin da zai sā ni in shiryu, in bi umurnin kitābinka. 
Kā san abun da yake tāre da ni, yā Ubangijina, amma nī, ban san abun dake tāre da kai ba. Kai nē ƙadīran masani.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Yabo (#11725)

Martaba ta tabbata ga sūnanka, yā Ubangiji Allāna! Kai nē wanda kōmi da kōwa yake bautāma, amma bā ka bautāwa kōwa, kai nē mamallakin kōwa da kōmi, amma bābu mai mallakarka. Kai nē masanin kōmi da kōwa, amma kā fi ƙarfin a san kōmi nāka. 
Da ka sō mutane su san ka, sai da kalmarka guka ɗaya, ka rāya dūniya, kuma ka halicci duk abun dake sama da ƙasa. Bābu wani Allah sai kai, mahalicci, mai rāyāwa, maɗaukaki mabuwāyi.
Ina rōƙon ka, da wannan kalma da kā sauko daga irādarka, ka bā ni izinin shan ruwan nan rāyayyu, da ka rāya zukācen zāɓɓaɓun bāyinka, ka wanke rūhun māsu ƙaunar ka, in sāmu īkon mayar da fuskāta wajenka, kullum, kuma cikin kōwane hāli.
Kai nē Jalla sarkin sarauta, mayalwaci. Bābu wani Allah illā kai, mai shirya kōmi, maɗaukaki masani.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

