Wa’azi (#11737)

Yā Allah, ka būɗa ƙōfa, ka bāda hāli, ka sā hanya ta zama shiryayya, ka tsāga daji, don mu sāmu jagōra har zuwa wajen waɗannan rāyukan da ka shirya zukacensu zuwa ga addininka, kuma dā dai ka tūro su wajenmu. Kai nē rāhimi mayalwaci, mabuwāyi.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Wa’azi (#11738)

Sūnanka ya girmama yā Allāna. Yanzu da ka sā ni hanyar gāne gaskiya, ina rōƙon ka, daga sūnanka wanda ya fi ƙarfin a kwatamtā shi da harshe kō da rubūtu, sūnanka wanda ka ɓōye har abadin ābāda, kuma wanda zā a rika ɗaukakāwa har kullum, ina rōƙon ka sā, nan da ƙārēwar shēkarar nan, tūtar īkonka ta ƙāra hayēwa, dūniyar nan ta wadāta da arzikinka, ta dukufa cikin fargā da hanyar saninka da kusanta da kai, kuma kōwa ya tāshi tsaye don ya bāda wa’azin addininka. Lalle, kai nē mabuwāyi, mai girma, karīmin, mai kōmi, kuma mai aikata abun da yake sō.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Wa’azi (#11739)

Yā Allah Ubangijina! Kō da yake nī bā kōwa nē ba, kuma bā ni da wata gwaninta, gā ni ɗauke da haramar aikata babban abu, sabōda nā ɗauki niyar baza kalmarka, kuma nā shirya wātsa addininka cikin dūniya gabāɗaya. Nā san sarai, bā ni da ƙarfin cika wannan aiki, in bā kai ka taimakē ni ba da rūhu mai tsarki. Ka bā ni nasara da taimakon malā’ikunka na samāniya, ka sauko mani īkonka, wanda yake maida ƙuda ya zama shirwa, ɗason ruwa ya zama tabki har mā ya zama tēku, ƙwāyar ƙasa ta zama tarmāmuwa mai haske.
Yā Ubangiji, ka shirya ni da īkonka mai nasara, kuma da ƙarfinka mai rātsa kōmi da kōwa, don harshēna ya iya yaba ka, kuma ya maka kirāri cikin halittarka, don kuma zūciyāta ta cika da ƙaunarka, kuma da saninka.
A gaskiya, ka na da īkon yin abunda ka ga dāma, mulkinka yā mallaki kōmi da kōwa.

-`Abdu'l-Bahá
-----------------------

Wa’azi (#11740)

Ya kai Allah, mafi kwatamci, yā kai Ubangijin tālikai! Rāyukan nan sū ne jāruman nan nāka na samāniya. Ka dāfa musu, yanda da taimakon malla’ikun samāniyarka, zā su ci nasara. Ka sā kōwane rai, ya ciyō kan wannan karkara, da ƙaunar Allah, kuma da hasken wa’azin Ubangiji. Yā Allah ! Ka zama kai nē madōgari da mataimaki a garēsu cikin hamāda, tudunnai kō fadama, ƙunci kō shāya, kō tēku, ka amince da su, don su sā a ji kiranka a cikin hikimarka da īkonka.
A gaskiya, kai nē mabuwāyi, mai ƙudura, masanin kōmi, ƙadīran. Kai nē mai basīra, mai ji, mai gani.

-`Abdu'l-Bahá
-----------------------

