Kāriya (#11730)

Yabo ya tabbata a garēka, yā Allāna! Kai nē wanda daga būɗa bāki, sai duka dūniya ta yi gilgiza, wanda daga kurta alƙalaminka, ka rarraba bāyunka. Nā shaida yā Allāna, da cēwa, a wannan wahayi, kalmarka guda ɗaya tā sā duk halitta tā zama mai hallaka, kuma da wata kalmar, duk wanɗanda ka zāɓā, suka rāyu da sābuwar rāyuwa, dōmin alfurmarka da karāmarka. Sabōda haka, nike maka gōdiya da yabo, don darajar duk waɗanda kake ƙauna, waɗanda ka sāke rāyāwa da ruwa māsu rāyarwa, da suka ɓullo daga marmaron yardarka. 
Tunda yake, kā rāyar da su a cikin alhērinka mai girma, yā Allāna, ka sā hankalinsu ya kōma zuwa wajen umurninka. Da yake kā yarde musu, shiga cikin ɗākin addīninka, ka yarde musu a cikin alfurmarka, kada kōmi, ya riƙe su nēsa da kai. Ka būɗe mā zukācensu yā Allāna, ƙōfōfin saninka, don su gāne da kai nē wanda ya fi a gāne shi, wanda duk halitta ba ta isa ta farga da iyākacinsa ba, wanda yake yā wuce inda, kōmin ƙōƙarin bāyinka, su fahimta da yanda kake ciki, kuma ka wanke zukācensu, dōmin kada su kula da waɗannen maƙaryata, māsu yawan sūrūtu da suke ƙariyar batu da sūnanka.
Yā Ubangijina, ka bā bāyin nan nāka, hamzarin da zā su sarkafa a addīninka da kuzāri ta yanda har abada, bā zā su kula ba da habaicin wanɗanda ba su sā kōmi gaba ba, in bā abun dūniya ba, masu aikata abūbūwan da ka hana a cikin litattafanka da kitābanka. Kā san yā Allāna, ina jin kūkan kūrāyen da suke bayyana da kamannin bāyinka. Ka kāre masōyanka da sharrinsu, kuma ka yarda su riƙe abin da ka bayyana cikin wanan wahayi nāka wanda cikin saninka, ka ƙayyada cēwa, bā shi abōkin tārayya. 
Ka isar musu, yā Allāna, da abun cin mōriya, ka haske su da hasken saninka don su fahimta da kai nē sama ga kōmi, kuma su shaida da ɗaukakarka a bisa halittarka da nasararka ga waɗanda suke sama da na ƙasa. Ka na da īkon aikata kōmi, yanda ka ga dāma. Bābu wani Allah in ba kai ba. Kai nē jalla, wanda duk tāliki yake rōƙon taimakonka.
Yabo ya tabbata a garēka, yā kai Ubangijin tālikai.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Kāriya (#11731)

Yā Allāna, zukāce da yawa masu sanyi, sun zāzāfa kusa da gumin addīninka. Hankulla da yawa masu gyangyaɗi, sun wartsake da suka ji zāƙin muryarka. Sabbin zuwa da yawa, sun nēmi mafaƙa a ƙalƙashin ɗayantakarka. Ma jī ƙishirwa da yawa, sun nēmi ɗanɗana ruwan rījiyarka mai rāyarwa, a wannan rānar rānaikunka!
Alhēri ya tabbata, ga wanda ya juya fuskarshi wajenka, kuma ya gaugauta, don ya iske tarmamuwar sāhiyar hasken huskarka.
Alhēri ya tabbata, ga wanda a bisa hanyarka ya ɓatar duk dūkiyar da ka mallakar masa a cikin kyautarka ta wajen taimako.
Alhēri ya tabbata, ga wanda don tsananin ƙaunar ka, ya yi wātsi da duk wani abu da bā kai nē ba.
Alhēri ya tabbata, ga wanda dōmin murnar sāduwa da kai, ya rabu da sarkafa da kōmi in ba kai ba.
Ina rōƙon ka, yā Allāna, da wanda shīnē sūnanka, kuma cikin īkonka, ya tāshi sama daga kurkukun da yake ciki, ka ƙaddarāwa kōwa, abun da kake sō.
A gaskiya, ƙudurarka ta wuce gwalgwado da kōmi.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Kāriya (#11732)

Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangiji Allāna. Ga bāwanka, wanda a cikin hannunka, ya shā ruwan rahamarka, kuma ya ɗanɗana dāɗin ƙaunarka a wannan rānā wadda take tāka. 
Ina rōƙon ka, don darajar bayyana sunāyenka, ka kāre shi da duk wata darūra da zā ta hana shi ƙaunar ka, kō ta kaudar da fuskarshi daga kallonka; ka kāre shi, ta yanda randunōnin māsu sakaci su kāsa kaucar da shi daga hanyar jin dāɗinka. Ina rōƙon ka bā shi arzikinka, kuma ka ɗaukakā shi yanda zā ya hangi dūniya, ya gāne da abu cē mai wucēwa kamar ƙibtar ido. A cikin īkonka marar iyāka, ka kāre shi da duk abun da kake ƙyāma.
A gaskiya, kai nē Ubangijinsa, kuma Ubangijin duka tālikai.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Kāriya (#11733)

Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangiji Allāna! Gā ni ina nēman tarbon irādarka, kuma nā nufā wajen kujērar alfurmarka. Nī nē wanda na yi wātsi da kōmi, na nufi ƙalƙashin kāriyarka, na jūya fuskāta wajen munbārin bayyanarka da zauren ɗaukakarka. 
Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, don kiranka wanda ya sā waɗanda suka bāda gaskiya ga ɗayantakarka, kuma suka zābura nēman tsīra ƙalƙashin rahamarka, kiranka da ya sā māsu ciki ɗaya, suka yi nēsa da kansu, kuma suka yō wajen sūnanka mai girma, wanda ta wajenshi āyōyinka suka sauko, alkawalinka ya cika, shaidarka ta tabbata, haskenka ya bayyana, gaskiyarka ta tabbata, alāmunka ya huto hīli.
Ina rōƙon ka sā ni cikin waɗanda ka ƙilga da su, shan ruwan hannuwanka, ruwa māsu rāyarwa da rāyuwa ta gaske, ka kuma sā ni cikin waɗanda suka yi wātsi da kōmi nāsu, kuma suka nufi wurinka, waɗanda suka wadāta da baiwarka marar iyāka, kuma lēɓunansu nā riƙe da yabonka, zukācensu ɗauke da tunāninka, suka gaugauta zuwa ga hīlin shuhāda.
Ina rōƙon ka, yā Allāna! Ka saukar mani da abunda zai rabā ni da duk wani abun da bā kai nē ba, kuma ka kāre ni daga sharrin maƙiyanka waɗanda suka ƙi bāda gaskiya ga alāmunka. Kana da īkon aikata abunda kake sō.
Bābu wani Allah illa kai, mai taimako cikin hallaka, mai rāya kansa da kansa.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Kāriya (#11734)

Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangiji Allāna, nī nē bāwanka wanda ya sarƙahu ga igiyar rahamarka. Ina rōƙon ka, da sūnanka wanda ya mallaƙi kōmi, a cikin waɗanda ake gani da na ɓōye, sūnanka wanda daga shīnē, rāyuwar gaskiya ta bayyana bisa kōmi da kōwa. Ka ƙarfafā ni a cikin mulkinka wanda ya wanzama sama da ƙasa, kuma ka kāre ni da duk wata cūta kō wahala.
Nā shaida cēwa, kai nē Ubangjijin duka sūnāye, mai yancin umurtar duk abun da yake gani daidai nē a garēshi. Bābu wani Allah illa kai, mabuwāyi, masanin duk abun dake ɓōye, mai basīra.
Ka ƙaddaro mani, yā Ubangijina, abun da zai zama mai alhēri nē a garēni dūniya da lāhira. Ka sā ni cikin alkawarin da ka mā zāɓaɓɓun bāyunka, waɗanda ban tsōron munāfikai, tankiyar kāfirai kō duhun ran waɗanda suka nīsanta da kai, ba su hanā su ba jūyāwa zuwa  garēka.
A gaskiya, kai nē mai taimako cikin hallaka da girman mulkinka. Bābu wani Allah in bā kai ba, maɗaukaki, mabuwāyi.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

