Dare (#11714)

Ta yāyā zan nēmi barci, yā Allah Ubangijina, alhāli kuwa, ina ganin wanɗanda suke ƙaunar ka, bā su rumtsāwa don tsananin tsōron su yi nēsa da kai, kuma, ta yāyā zan mīƙē, in nēmi hūtū a kan gā shi ina ganin rāyukan māsu ƙaunar ka, suna kūkan sun yi nēsa da kai?
Yā Ubangijina, nā damƙa rūhūna da duka gabāɗayāna a hannun dāmar ƙudurarka da kāriyarka. A cikin sō da yardarka nē, idan na kwanta nike aje kaina, kuma nike ɗagā shi.
A gaskiya, kai nē mai kārēwa, wanda yake tsaye bisa kōmi, mabuwāyi, ƙadīran. Ina barci, kō ina falke da īkonka, bā wani abun buƙātāta, illā abin da kake so. Nī bāwanka ne, ina cikin hannuwanka. Ka taimakē ni cikin rahamarka, in aikata abūbūwan da zā su baza ƙamshin ƙaunarka.
Bā shakka, da ni da duk wanɗanda suke ƙaunar ka, gūrinmu kēnan. Yabo ya tabbata a garēka, yā Ubangijin tālikai.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Dare (#11715)

Yā Allāna, majibincīna, maƙārashin duk wata bukātāta ! Gā bāwanka nan yana niyyar ya rumtsa a cikin inuwar rahamarka, yā kwanta ƙalƙashin samāniyar alfurmarka, yana rōƙon umurninka da tsarinka.
Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, da idonka wanda bā ya rumtsāwa, ka hana idānuwāna dūbin wani abu, in bā kai ba. Ka ƙarfafa ganīna, ta yanda zan tsinkāyi alāmunka, kuma in yi shāwar kallon wahayinka. Kai nē wanda tabbatar ƙadīrarka ta gētse duka tūshen mulki. 
Bābu wani Allah illā kai, mabuwāyi, mai nasara, marar iyāka.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Dare (#11716)

Yā Ubangiji, nā jūya huskāta wajen fādar ɗayantakarka, kuma nā nutsa kaina cikin tēkun rahamarka. Yā Ubangiji, ka wāye idānuwāna cikin wannan duhun, don tsinkāyen haskenka mai cikakken haskēwa, ka mayar da ni maji dāɗi a wannan zāmani mai abun al’ajabi ta wajen ɗanɗanon ƙaunarka.
Yā Ubangijina, ka sā in ji kiranka, ka kuma būɗe mani ƙōfōfin arshinka, dōmin in ga annurin ɗaukakarka, ta yanda zā ta huzgē ni zuwa wajenka.
Lalle, kai nē mai bayyanarwa, karīmin, mai rahama, mai yāfēwa.

-`Abdu'l-Bahá
-----------------------

