Aure (#11705)

Shīnē mai yalwa, mai kyauta ! Yabo ya tabatta ga Allah, mai dawwama, maras sauyāwa, maras gōcēwa, mai rayuwa har abada, wanda zātinsa yake shaidar cēwa, haƙīƙan, Shī kaɗai yake, bā Shi abōkin tārayya, mai ƴanci, mafi girma ! A gaskiya, mun shaida cēwa, bābu wani Allah illa Shi, mun yarda da kaɗaitakarsa, kuma mun tabbata da ɗayantakarsa, bā wani Allah sai Shi. Har kullum, Yā wuce gaban a kai garēshi, girmanshi bā ya da iyāka, kuma yā fi ƙarfin kwatamci.
A lōkacin da Ya sō bayyana alfurmarsa da alhērinsa zuwa ga mutane, kuma dōmin Ya tsāra dūniya, sai ya sauko umurni, kuma ya kafa dōkōki. Cikin waɗannan dōkōki, akwai aure da Ya maida shi tamkar gārun jin dāɗin rāyuwa da tsīra, daga samāniyar tsarkakarsa, Yā rubuta wannan dōka cikin Littāfi Mafi Tsarki. Ya cē, ɗaukaka cē mai girma : « Ku yi aure dōmin ku haifi wanda zai tuna mani bāyūna. Wannan ɗaya nē daga cikin umurnīna, ku bī shi don jin dāɗin rāyuwarku ».

-Bahá'u'lláh
-----------------------

Aure (#11706)

*Ginshiƙin aure a cikin addinin baha’i shīnē, haɗin kai da shiri tsakānin ango da amarya. Amma, yā cancanta su yi hattara matuƙa, kuma su kōyi bin hanyar sanin jūna da kyau. Yā kamata wannan igiya wadda bā ta cirēwa, ta danganta bisa ma’āmala mai ƙwāri, dōmin shinfiɗa shiri, aminci da haɗin kai, sabōda kaiwa ga rāyuwar har abada.
*Abdul’Baha
*Kamar yanda Allah ya umurto cikin Kitābil Aƙdas (Littāfi Mafi Tsarƙi), dōmin a ɗaura auren, yā cancanta ango da amarya, su karanta wannan āyā gaban wakīlan majalasar tara :
*Ango ya cē :

*« A gaskiya mun dōgara ga nufin Ubangiji Allah »

*Amarya ta cē :
*« A gaskiya mun dōgara ga nufin Ubangiji Allah »
 

Shīnē Allah ! Yā Ubangiji mafi kwatamci ! Cikin basīrarka maras iyāka, kā umurci yan adam da yin aure, dōmin zūriyarsu ta bi mā jūna cikin wannan dūniya mai ƙārēwa, kuma har kullum, su rāyu cikin ibāda gaban fādar kaɗaitakarka, suna rōƙo da yabonka, cikin sūjada, da hamzarin bauta maka.
*«Allah yā halitto rūhunnai da mutāne don su yabā shi»
Don haka, ka haɗa, cikin samāniyar rahamarka, waɗannan tsuntsāyen gidan ƙaunarka, kuma ka sā, su zauna wurin da alhumarka zā ta dinga saukōwa, ya zamanto daga haɗuwar waɗannan tēkun ƙauna, ƙōramar sōyayya ta halitto zūriya mai kiyāwon lu’ulu’u, da zā ta ɓullo ta fito hīli.
*«Yā garwaya tēku biyu suna haɗuwa. A tsakāninsu, yā kurta iyāka da bai cancanta ba su ƙētare. Waɗanne daga cikin ni’imōmin Ubangijinku zā ku wātsar ? Ya nā fitar daga kōwannensu, lu’ulu’u manyā da ƙanānā.»
Yā kai Ubangiji mayalwaci ! Ka sā kyaukyāwar haifuwa ta sāmu daga wannan aure.
Kai nē bā shakka, mabuwāyi, mafi girma, mai gāfara da bā ta da iyāka.

-`Abdu'l-Bahá
-----------------------

