Arwalla (#11703)

*Kana wanke hannuwa, ka cē :
Yā Allah, ka bā hannuwāna ƙarfi da īkon ɗaukar kitābinka; kada kōmi ya sā su falgaba. Kaucē su da shiga abinda bai shāfē su ba. A gaskiya, kai nē mai īko, ƙadīran.

*Kana wanke fuska, ka cē :
Nā juya fuskāta wajenka, yā Ubangijina. Hanā ta da kula da kōmi bāyan kai, kuma ka haske ta da annurinka mai ni’ima.

-Bahá'u'lláh
-----------------------

